SHAPES NA FUSKA


Sanin shape din fuskarki shixai taimakamiki wajan tsara kwalliya data dace da irin wannan fuskar. Kowane mutum akwai shape din fuskarsa, Wanda idan masu shapes din fuska daban daban sukace xasukwaikwayi irin kwalliyar me wani kalar shape din, to axahirin gaskiya kwalliyar baxatahau xaxauna tayi yadda akesoba.

Kalolin Shape din fuska sun hada da:

  1. oval shape
  2. long shape
  3. Round shape
  4. square shape
  5. heart shape
  6. Diamond shape


Wadannan sune shapes damuke dasu na fuska. Kuma saninsu xaitaimakawa mace wajen yin kwalliya kamar inxatai contouring da shafa blush ko jagira yadda zasu fito suyi das a fuska kamar an manna su.

Zaki iya tantance ya shape din fuskarki yake tahanyar tsayawa cak fuskarki tana kallan mudubi, saikisamu wani Abu daxaki diddiga ajikin mudubin kamr jagira komaka, kibi shape din fuskartaki tahanyar diddigawa. To inkin xagaye fuskarki da dige dige ajikn mudubin xakiga yadda shape din fuskarki yake.

 

GYARAN FUSKA

  • tumatir
  • madara

ki kwaba madara da tumatir sai ki shafa tsawon minti talatin sai ki wanke
 

2.garin alkama

  • zuma
  • madara

ki hada su ki rinka shafawa kafin ki shiga wanka
3

  • .lemon tsami
  • zuma

ki hadasu idan zaki kwanta ki rika shafawa idan zaki kwanta da safe ki wanke da ruwan dumi
 

  • 4.man ridi
  • man kwakwa
  • man habba
  • miski

ki hada mayukan sai ki diga turaren miski ki rinka shafawa yana sanya fata tayi laushi da santsi

 

 

GYARAN FUSKA 2

amare da dama suna fama da matsalar kurajen fuska musamman farar mace Wanda sune sukafi fuskantar wannan matsalar

Zanyi bayanin hanyoyi goma Wanda amarya zatabi don magance matsalar kurajen fuska

 

(1) Da farko ana so awa biyu ko uku kafin ki kwanta barci sai ki shafa man goge baki a fuskarki, musamman wuraren da kurajen pimples suke da yawa.
Ba kowane irin man goge baki za ki shafa ba, ana so ki shafa farin man goge baki ne. Idan kin ga dama za ki iya wanke fuskarki idan man goge bakin da kika shafa ya kai minti 30, idan kin ga dama kuma za ki iya kwantawa da shi har zuwa wayewar gari. Za ki rika maimata hakan har zuwa wadansu kwanaki, idan kin yi hakan za ki ga canji a fuskarki.


(2) Ki kasance mai yawan shan ruwa.yawaita shan ruwa ba wai zai sanya miki laushin fata ba ne kawai, a’a, zai taimaka miki wajen yaki da kurajen pimples din da suke fuskarki. Haka yana da kyau ki guji yawan cin abincin gwangwani, kasancewar suna dauke da wasu sinadarai da za su rika sanya kurajen fuska. Ya kamata ki yawaita cin ‘ya’yan itatuwa da suka hada da su abarba da lemu da ayaba da kankana da sauransu.


(3) Ki rika amfani da abin shafawar da ake kira ‘(Antiodident spray) irin su (Jane Iradale) da (Neutrogenia Rapid Clear) da (Acne Eliminating Spot Gel) da sauransu, hakan zai taimaka mikiwajen daidaita man da  ke fatarki, wanda masana fata suka ce idan ya yi yawa yakan haifar da kurajen fuska.


(4) Ki kasance mai amfani da man (Cornmeal) a fuskarki, yakan sanya kurajen fuska su motse sannan a hankali su bace, misali man shi ne, (Intagilo Clear Sal Cleanser.) Sannan ki rika amfani da man da ke hana yaduwar kwayar cutar bakteriya, irin wannan man yakan ratsa kofofin da suke fatar fuskarki da ma jikinki gaba daya, sannan yana yakar kwayoyin cutar da suke fatarki, a lokaci guda ya daidaita miki yawan man da yake fitowa daga fatarki. Zai kuma cire miki kwayoyin halittar da suka mutu a cikin fatarki. Misalinsu; (Phytomer Gommage) da Luffa-0.


(5) Yana da kyau ki ware wata rana ko wadansu ranaku a cikin mako ba tare da kin shafa kayan kwalliya a fuskarki ba, hakan zai bai wa fatar fuskarki samun ‘yancin shigar da kuma fitar da iska ta kofofinta ba tare da wani cikas ba. Haka idan za ki shafa kayan kwalliyar a fuskarki, to ki yi amfani da kayan kwalliyar da ba sa toshe kofofin fatar fuska.


(6) Ki kasance mai shafa mai domin fatar fuskarki ta kasance cikin danshi, kasancewar wadansu kurajen fuskar sun fi bata fuska idan fuska tana bushe.

(7) Yi amfani da man (Tea Tree’) domin ba wai kawai yana baje kurajen fuska ba ne, a’a yana rage karfinsu da kuma kalarsu. Za ki sami ire-iren wadannan man a shagunan sayar da kayan kwalliya na zamani.

(8) Ki kasance mai yin taka tsan- tsan wajen amfani da ire-iren man shafawar da kike amfani da su a gashin kanki, ma’ana kada ki sake ya rika taba fuskarki hakan zai iya haifar miki da kurajen fuska, kasancewar wadansu sinadaran an yi su don su taimaka wa gashin kai ne, don haka idan suka shiga kofofin fatar fuskarki, sai su haifar miki da matsala.

(9) Ki kasance mai gasa kurajen fuskarki: Duk lokacin da kurajen pimples suka fito miki sai ki samu wani kyalle mai tsafta, sai ki tsoma shi a ruwan zafi, ba wanda ya tafasa ba, bayan kin tsoma sai ki fito da shi, sai ki rika dora shi a kan wajen da kurajen suke, sannan ki rika gogawa a hankali, zafin kyallen yakan sa kurajen su motse daga nan su mutu.

(10) Ki guje yin amfani da hannunki wajen fasa kurajen da suke fuskarki, domin hakan yana kara yawansu hade da sanya fuskarki ta kara cabewa

 

DOMIN SAMUN LAUSHIN FUSKA DA MAGANCE KURAJE

 

.xaki shanya bawon lemon xaki dana kwai sai ki daka suyi laushi ki kwaba da ruwa kirika shafawa kafin ki shiga wanka

 

MAN SHAFAWA DON LAUSHIN JIKI

  1. man kwakwa
  2. man kade
  3. man angurya
  4. man xaitun
  5. almond oil
  6. baby oil
  7. madarar turare 
  8. cocoa buter

ki hada su duka ki rika shafawa jikinki xaiyi taushi sannan ki hada da sabulun

  • sabulun xaitum
  • tetmasol
  • sabulun salo da gana
  • sabulun karas
  • sabulun cocumber 
  • kurkur

ki hadasu ki rika wanka dashi amma sai anjure
ko ya kare ki siyo ki sake hadawa sannan ki rage shiga rana

 

GYARAN FUSKA TAYI SHEKI

 

Gyaran fuska tayi fari da sheki naturally batare da kinsa chemical a fuskarki ba. Sannan zanyi bayani akan matan da suke tsintar kansu da wani irin wari ko kuma wani baki-baki a cikin armpit dinsu(hammatarsu) ko bakin fuska daga gefe daya due to bleaching products or sunborn. Dafarko idan kika ga fuskarki na irin wannan duhun daga gefe ko kusa da idonki to cikin biyune kina shafa cream kina shiga rana ko kina shafawa lokacin gari da zafi.

 

Na biyu ko kina shafa man dayafi karfin fatarki to dai koma menene ya janyo ga hanyar da xakibi ki goge wannan tabo zaki sami madara ta ruwa kisata a fridge tayi sanyi sosai sai ki goga a wannan tabon naki bayan minti ashirin saiki wanke sannan idan gari da zafi zaki sami ruwan sanyi kisa cottonballs ki tsoma ki dora akan tabon saiki bari yayi minti 5 saiki cire cotton din ki shafa mai a fuskar.I dan kika yi sau uku saiki dinga yiwa fuskar gaba daya.Am assuring you zaki mamaki sosai.

 

WARIN HAMATA-waddata sami kanta da irin wannan warin ko bakin saita sami bakin soda tasa lemon tsami daya ta kwabata tashafa a hammatar har minti goma sha biyar sannan ta wanke intanayi kafinta shiga wanka zataga komai ya daidaita. NATURAL FACE WHITE- Idan kinaso fuskarki tayi fari batare da side effect ba saiki sami cinnamon powder da paste na gwanda ko kabewa da olive oil kadan kishafa a fuskarki kafin kishiga wanka insha Allahu inkika juriyin wannan fuskarki zata dinga fari kamar me bleeching..